IQNA

22:49 - October 10, 2019
Lambar Labari: 3484140
Bangaren kasa da kasa, a zaman da kwamitin tsaro zai gudanar yau, zai tattauna batun harin Turkiya a Syria.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a wani lokaci yau Alhamis ne ake san kwamitin tsaro na MDD, zai yi zama, bisa bukatar kasar Faransa kan farmakin da Turkiyya ta kaddamar kan kurdawa Siriya.

A jiya ne kasar Turkiyya, ta kaddamr harin sama dana kasa kan kurdawan arewacin Siriya, da take dangantawa da ‘yan ta’adda.

Tuni dai kasashen duniya sukayi tir da matakin sojin na Turkiyya, tare da umartar ta data dakatar da farmakin.

Yanzu haka dai kasashen Faransa, Jamus, da kuma Biritaniya, na shirin fitar da wata sanarwa ta bai daya, ta yi tir da kakkausar murya kan matakin na Turkiyya.

A nata bangare kuwa majalisar dokokin AMurka, ta ce shugaban kasar ta Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, zai dandana kudarsa akan wannan matakin da ya dauka, kan kurdawa kamar yadda dan majalisa repablicain,Lindsey Graham, ya sanar.

 

 

3848875

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: