IQNA

23:10 - October 15, 2019
Lambar Labari: 3484157
Bangaren kasa da kasa firayi ministan kasar Newzealand ta ce ba za ta taba lamuncewa da tsatsauran ra’ayi  a kasar ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin Yani Shafaq cewa, a yau firayi ministan kasar Newzealand ta ce ba za ta taba lamuncewa da tsatsauran ra’ayi  a kasar ba.

A lokacin da take Karin bayani kan kisan gillar da aka yi wa musulmi a cikin watan Maris da ya gabata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar musulmi 51 da kuma jikkatar wasu da dama, firayi ministan kasar Newzeland ta sha alwashin kawo karshen irin wannan tsatsauran ra’ayi a kasar.

Gwamnatin kasar dai ta dauki nauyin iyalan wadanda suka rasa rayukansu tare da daukar nauyin karatun ‘ya’yansu, kamar yadda kuma wadanda ba su da shedar zama dan kasa an basu takardun shedar zama ‘yan kasa a hukumance.

3849934

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: