IQNA

22:56 - October 21, 2019
Lambar Labari: 3484175
Bangaren kasa da kasa, ministan ma’aikatar kula da harkokin addini a Aljeriya ya yi rangadi a makarantun allo na garin Garadiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar ad rahoton cewa, a jiya Yusuf Bilmahdi ministan ma’aikatar kula da harkokin addini a Aljeriya ya yi rangadi a makarantun allo a daya daga cikin garuruwan kasar, inda ya cea  halin yanzu makarantun kur’ani a kasar sun kai dubu 25, kuma kimanin dubu 20 daga ickinsu gwamnati na kula da su.

Ya ci gaba da cewa wannan rangadi da yake yi shi ne karo na hudu, wanda kuma a cikinsa zai zagaya garuruwa daban-daban domin ganewa idanuns halin da makarantun allo suke ciki a fadin kasar.

Ministan ya ci gaba da cewa, akwai tsarin da suka bullo da shi, wanda a halin yanzu ana yin amfani da shi kusan mafi yawan makamarntun allo na kasar, wanda zai baiwa daliban dammar yin karatun kur’ani da kuma na zamani lokaci guda.

Ya kara da cewa za su ci gaba da bin kadun yanayin da makarantun kur’ani an allo suke ciki a  kasar, tare da karfafa su da kuma basu dukkanin taimakon da suke bukata.

3851374

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: