IQNA

22:55 - October 24, 2019
Lambar Labari: 3484185
Bangaren kasa da kasa, kotun Isra’ila ta wanke daya daga cikin yahudawan da suka kashe wasu iyalan Falastinawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin bawwaba News cewa, a jiya kotun Isra’ila ta wanke daya daga cikin yahudawan da suka kashe wasu iyalan Dawabisha a garin Nablus da ke arewacin gabar yamma ta kogin Jordan.

Kotun ta ce a halin yanzu wannan bayahude zai iya tafi har sai lokacin da ta ga akwai bukata za ta kiraye shi.

Kimanin shekaru hudu da suka gabata ne wasu gungun yahudawa masu tsatsauran ra’ayi suka kai hari kan gidan Dawabisha, inda suka banka ma gidan wuta, kuma yak one kurmus.

A harin sun kashe mai gidan da matarsa da yaransa dan watanni a8 da haihuwa, yayin da kuma daya daga cikin yaran ya samu raunuka sakamakon kunar wuta.

 

 

3852264

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: