Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, cibiyar musuunci ta birnin Lanadan ta sanar da cewa, a ranar Lahadi mai zuwa za a gudanar da taron tunawa da ranar wafatin manzon Allah da shahadar Imam Hassan wanda yay i daida da ranar 28 ga watan Safar, inda Sayyid Hashem Musawi zai gabatar da jawabai.
Za a fara taron na tunawa da ranar wafatin manzon Allah (SAW) da shahadar Imam Hassan (AS) zai gudana ne daga misalign karfe 19:45 na yammacin ranar ta Lahadi.
Haka nan kuma wannan cibiyar za ta gudanar da wani zaman taron na tunawa da zagayowar ranar shahada Imam Rida (AS) a babban ginin cibiyar da misalign karfe 19:45 na dare 30 ga watan Safar.