IQNA

Wani Mai Kyamar Musulmi A Birtaniya Ya Amsa Laifinsa

22:48 - October 27, 2019
Lambar Labari: 3484197
Wani mutum da ya shahara da yada kiyayya da kyama kan musulmi a Ingila tun bayan harin Newzealand ya amsa lafinsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga CPS cewa, wannan mutum ma shekaru 38 da haihuwa ya shahara da yin izgili da cin zarafi ga muuslmi a yankin West Minister, tun bayan harin Newzealand tare da nuna goyon bayansa kan harin.

Bayan gurfanar ad shia  gaban kuliya ya amsa cewa shi ne yake cin zarafin musulmi a cikin jirgin kasa a yankinsu da ke kusa da birnin Landan, kamar yadda yake tunzura jama’a domin su yamaci musulmi.

Da farko dai kotu ta yanke masa hukuncin biyan tara ta fan 200, amma daga bisani kuma kotun ta ninka tarar inda aka kara masa 200, kudin suka zama fan 400, kuma za a saka wannan a cikin tsarin bayanansa a matsayinsa na dan kansa.

 

3852660

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha