IQNA

23:09 - October 28, 2019
Lambar Labari: 3484198
Ma’ikatar kula da harkokin addini a masar ta sanar da cewa, ana shirin gudanar da wani taro mai taken manzon Allah (ASWA a cikin kur’ani.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ma’ikatar kula da harkokin addini a kasar Masar ta sanar da cewa za a gudanar da taron karawa juna sani  mai taken manzon Allah (ASWA a cikin kur’ani a masallacin Sayyida Zainab da ke birnin Alkahira.

Bayanin ya ce malamai da masana daga sassa na kasar za su halarci taron, da suka hada da sheikh Sheikh Nuh Alisawi mataimakin ministan ma’aikatar kula da harkokin addini, sheikh Muhammad abubakar limamin masallacin Zainab (AS) shikh Hazim Jalal Alqiyqdi daga ma’aikata kula da harkokin addini, da dai sauransu.

Taro wanda za a fara a gobe Talata, zai mayar da hankali wajen yin dubi kan ayoyin kur’ani da suka ambaci manzon Allah kai tsaye, da kuma bayyana matsayinsa da kyakyawan dabiunsa.

 

3852919

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، shirin ، harkokin addini ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: