IQNA

21:30 - November 02, 2019
Lambar Labari: 3484214
Musumin Faransa sun yi tir da kalaman batunci da ministan harkokin cikin kasar ya yi kan muslucni.

Kamfanin dilalncin labaran IQNA, shafin jaridar Yaum sabi ya bayar da rahoton cewa, Christophe Castaner ministan harkokin cikin gida na kasar Faransa ya bayyana cewa, tsaida salla da kuma tsaida gemu, suna daga cikin alamun ta’addanci.

Abdullah Zekri mamba a kwamitin shawara na musulmin kasar Faransa ya mayar da martani da cewa; kalaman na ministan harkokin cikin gidan kasar ta Faransa abin kunya ne, domin kuwa tsaida gemu abu ne wanda kowa yana yi musulmi da wanda ba musulmi ba, kamar yadda kuma tsayar da salla aikin ibada ne na musulmi baki daya, wanda kuma musulmi ne ma ayyukan ta'addanci suka fi cutarwa.

Wannan furuci na ministan harkokin cikin gidan kasar Faransa ya fuskanci martani a cikin fushi daga musulmin kasar Faransa da ma kasashen turai da dama, tare da bayyana hakan a matsayin karfafa gwiwar ayyukan nuna kiyayya ga musulmi a cikin Faransa da ma kasashen nahiyar turai.

 

3853890

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: