IQNA

21:53 - November 04, 2019
Lambar Labari: 3484223
Sojojin Amurka sun koma sansanoninsu da suka bari a arewacin kasar Siriya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayyana cewa sojojin na Amurka sun bar sansanoninsu a arewacin kasar ta Siriya ne jim kadan kafin sojojin Turkiyya su kutsa cikin yankunan arewacin kasar ta Siriya.

Amma a jiya Asabar sojojin na Amurka kimani 30 sun koma sansanoninsu dake yankin Jazira daga yammacin garin Raqqa a cikin lardin hasaka kusa da kan iyakokin kasashen Siriya da Turkiya.

Hakama an ga sojojin na Amurka suna sake tada sansaninsu da ke garuruwan Sarrin da kuma Sabit a ranar jumma’a da ta gabata. Banda haka anga mutocin yaki masu sulke na sojojin Amurka a wadannan yankuna suna sintiri a kusa da rijiyoyin man fetur a arewa maso gabacin kasar ta Siriya.

Sojojin kasar Turkiyya sun kutsa cikin kasar Siriya ne a ranar 9 ga watan Octobann da ya gabata, don samar da wani yanki a arewacin kasar ta Siriya don maida yan gudun hijirar kasar a cikin yankin da kuma korar mayakan kungiyar YPG wadanda ta dauke su a matsayin yan ta’adda, wadanda suke aiki tare da kungiyar kurdawa masu son ballewa daga kasar ta Turkiya.

 

3854817

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، aiki tare ، gudun hijira ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: