IQNA

23:09 - November 06, 2019
Lambar Labari: 3484228
Bangaren kasa da kasa, ma’ikatar tsaron kasar Faransa ta sanar da halaka jagoran wata kungiyar ‘yan ta’adda a Mali.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na News ya nakalto daga ma’ikatar tsaron kasar Faransa cewa, an halaka daya daga cikin  jagororin wata kungiyar ‘yan ta’adda a Mali mai suna Suna Nusrat Islam wal Muslimin.

Bayanin ya ce an kai wani hari ne kan ‘yan ta’addan ne a ranar 9 ga watan Oktoba inda aka halaka Ali Maichu.

Wannan kungiya dai tana kaddamar da hare-hare kan sojojin kasar Mali da na majalisar dinkin duniya da kuma na kasar Faransa.

Majalisar dinkin duniya ta ce Maichu yana da alakada Daesh da kuma alkaida, a kan haka aka saka sunansa cikin wadanda ake nema.

3855182

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، haka ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: