IQNA

23:12 - November 06, 2019
Lambar Labari: 3484229
Daga karshe dai bayan kwashe shekaru fiye da hudu Saudiyya na yaki a Yemen a yanzu ta amince ta shiga tattaunawa da ‘yan Huthi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, gwamnatin kasar Sudia ta bada sanarwan cewa ta na cikin tattaunawa da kungiyar Ansarullah wacce take iko da kasar Yemen don kawo karshen yakin da suke fafatawa tun kimanin shekaru biyar da suka gabata.

Wani babban jami’in gwamnatin kasar ta Saudiya ya fadawa yan jaridu kan cewa gwamnatin kasar bata taba rufe kofar tattaunawa da kungiyar Huthi ko Ansarullah ba, Sannan kasar Saudia a shirye take a kawo karshen yakin.

Kafin haka dai kungiyar Ansarullah ta sha nanata cewa tana son a kawo karshen yakin, amma sai idan gwamnatin kasar Saudia ta dakatar da hare-haren da take kaiwa kan mutanen kasar a matsayin sharidin shiga tattaunawa da ita.

Tun cikin watan Maris na shekara ta 2015 ne gwamnatin kasar Saudia da kawayenta suka farwa kasar Yemen da yaki, da nufin maida Abdu Rabbu Mansur-Hadi, tsohon shugaban kasar, kan kujerar shugabancin kasar.

Gwamnatin Saudiyya ta amince ta shiga tattaunawa da ‘yan Huthi ne biyo bayan munanan hare-haren da suka kai mata a kan babban kamfaninta na mai, da kuma kame dubban sojojinta a baya-bayan nan.

 

3855214

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، baya-bayan ، sojojinta ، Yemen
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: