IQNA

23:55 - November 11, 2019
Lambar Labari: 3484242
Babban sakataren Hizbullah ya bayyana cewa ba za a lamunce wa shigar shugular Amurka cikin Harkokin Lebanon ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna, babban magatakardar Kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sayyid Hassan Nasrallah wanda ya gabatar da jawabi a ranar tunawa da shahidan kungiyar a yau Litinin a birni Beirut, ya yi ishara da cewa a rana irin wannan ce; Shahid Ahmad Qasir ya kai hari akan sansanin ‘yan mamaya na sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila a garin Sur, tare da tarwatsa shi baki daya tare da kashe ‘yan mamaya.

Sayyid Nasarallah ya kara da cewa; Har yanzu abinda ya faru a wancan lokacin yana da muhimmanci a tahirin fito na fito da ‘yan mamaya. Shugaban kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce; Shahidai su ne wadanda su ka ba mu nasarorin da mu ka samu, don haka a duk lokacin da muke tunawa da su, muna tunawa ne da yadda muka ‘yanto da kasarmu ne daga mamaya.

Sayyid Nasarallah ya kuma ce; Karfin da muke da shi a yanzu wanda yake iya bamu damar fuskantar haramtacciyar kasar Isra’ila, ya samo asali ne daga sadaukar da kai na shahidai.

Dangane da zagayowar lokacin mauludin manzon Allah (s.a.w.) kuwa shugaban kungiyar ta Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah ya mika sakon murna ga dukkanin al’ummar Musulmin duniya.

 

 

3856412

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: