Kamfanin dillancin labaran IQNA ya nakalto daga shafin Egypt Today cewa, Shaqi Allam babban mai bayar da fatawa a kasar Masar ya a fadi ajiya 16 ga Nuwamban 2019 cewa, addinin muslunci addini ne na zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai.
Ya ce ya zama wajibi a karfafa duk wani abin da zai kawo zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai na duniya.
Shaqi Allam ya ce yada fahimtar juna a tsakanin maiya addinai, shi ne zai kawo zaman lafiya da ci gaban dukkanin al’ummomi.