IQNA

15:41 - November 18, 2019
Lambar Labari: 3484251
Daya daga cikin mahalarta taron makon hadin kai daga kasar Ghana ya bayyana cewa mazhabar iyaln gidan manzo na bunkasa a Ghana.

Shekh Muhammad ustafa Ya Jamal daya daga cikin mahalrta taron makon hadin kai da aka gudanar karo na 33 ya bayyana cewa, ana samun gagarumin ci gaba ta fuskar bunkasar mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar ta Ghana, idan aka kwatata da sauran lokutan baya.

Ya hakika akwai ci gaba a dukkanin bangarori ta fuskar bunkasar addinin muslunci a kasar Ghana, kamar yadda uma mazhabar ahlul bait take samun magoya baya a koina a tsakanin musulmi.

Dangane da masu bata sunan addinin musunci da sunan jihadi ko ain ya yi kama da haka kuwa, malamin ya ce wadannan kungiyoyi irin su daesh da masu dauke da irin akidunsu, ba su wakiltar addinin muslunci, kamar yadda uma basa wailatr al’ummar musulmi, domin kuwa abin da suke ba koyarwar musulunci ba ce.

Daga karshe ya jaddada kira ga dukkanin al’ummar musulmi kan wajabcin samun hadin kai a tsakaninsu, domin ta haka ne kawai za su zama masu izza da daukaka a duniya da ma lahira..

3857491

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: