IQNA

15:47 - November 18, 2019
Lambar Labari: 3484253
Bangaren kasa da kasa, wata cibiyar kare hakkin bil adama ta fitar da rahoto kan rusa gidajen falastinawa da Israila ke yi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ta bayar da rahoton cewa, a cikin bayani da da ta fitar, cibiyar kare hakkin bil adama a Falastine ta bayar da cikakken rahoto kan rusa gidajen falastinawa da Isaila ke yi a yankunan gabashin birnin Quds a tsakanin shekarun 2004 zuwa 2018, inda rahoton ya nuna cewa a cikin 2019 adadin ya ninka.

Bayanin ya ce, daga shekarar 2004 ya zwa yanzu Isra’ila ta rusa gidajen falastinawa guda 964 a gabshin birnin Quds, kamar yadda kuma ta mayar da falastinawa dubu 3 da 118 ‘yan gudun hijira a wadanan yankuna.

Tun daga shekara ta 1967 ne dai yahudawa suka fara mamaye yankunan falastinawa a yankunan gabar yamma da kogin Jordan, inda ya zuwa yanzu sun mamaye yankin baki daya.

Haka nan kuma yankunan gabashin quds wadanda majalisar dinkin duniya ta tababtar da cewa mallakin falastinawa wani baya da haki a kansu, amma Isra’ila tana ci gaba da mamae yankin tare da gina dubbn matsugunan yahudawa yan share wuri zauna.

3857818

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: