IQNA

22:32 - November 22, 2019
Lambar Labari: 3484264
Sayyid Abbas Musawi kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana furucin turai kan masu barna a Iran da cewa munufunci ne.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a yau Sayyid Abbas Musawi kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya fadi cewa, maimakon nuna goyon baya ga mabarnata a Iran, da zai fi kyau ga kasashen turai su cika alkawullan da su ka daukarwa Iran.

Ya ce abin da turawa suke nunawa kan goyon bayan masu zanga-zanga da barnata kaddrorin gwamnati da na jama’a da bankawa gidajen mai wuta da motocin bas bas masu daukar jama’a, hakan ya yi kama da munafunci.

Ya kara da cewa maimakon hakan da zai fi kyau su aiwatar da dukkanin abubuwan da suka yi alkawali a cikin ayrjejeniyar da suka cimmawa da Iran, wanda har yanzu ba su aiwatar ba.

 

3858659

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، barna ، Iran ، turai
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: