Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, hukumar kula da harokin ilimi da al’adu ta duniya UNESCO ta nuna cikakken goyon bayanta kan kare wuraren tarihi na Quds na falastinawa.
Bayanin ya ce wannan taro da UNESCO ta gudanar ya samu halartar ministocin ula da harkokin al’adu na kasashe 120 naduniya wadanda dukkaninsu sun nuna goyon bayansu ga wannan mataki.
Bisa ga bayanin da ministocin suka fitar sun jaddada cewa, birnin Quds na falastinawa ne kamar yadda yake a cikin kudirin majalisar dinkin duniya.
A cikin shekara ta 1981 majalisar dinkin duniya ta saka tsohon birnin quds da ke gabashin birnin a yanzu a cikin wuraren tarihi na duniya, amma a cikin 1982 majalisar ta bayyana yankin da cewa yana cikin hadari.