IQNA

23:09 - November 25, 2019
Lambar Labari: 3484272
Bangaren kasa da kasa, musulmi a  wasu yankunan kudu maso yammacin Najeriya sun bukaci a kara yawan kotunan muslunci.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya nakalto daga shafi Allafrica cewa, musulmi a  wasu yankunan kudu maso yammacin Najeriya da suka hada da Oyo, Osun, Ogun, Ekiti, Lagos, sun bukaci a kara yawan kotunan muslunci a cikin jihohin.

Musulmin wadannan jihohi suna cewa, samar da irin wadannan kotuna zai taimaka ma musulmi wajen warware da dama daga cikin matsalolinsu na zamantakewa, ta hanyar addini.

Haka nan kuma cibiyar kare hakkokin musulmi ta yankin ta ce dole ne a bar mata su rika saka hijabi domin kundin tsarin mulkin Najeriya bai hana yin haka ba.

3859466

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: