IQNA

18:09 - November 26, 2019
Lambar Labari: 3484273
Miliyoyin mutane ne suka fito domin nunaa rashin amincewa da ayyukan barna da sunan zanga-zangar korafi.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a jiya Litinin ne miliyoyin mutanen birnin Tehran anan Iran su ka gudanar da Zanga-zangar yin tir da kone-konen da wasu tsirarun mutane su ka yi a makon da ya shude.

Masu Zanga-zangar sun fito daga unguwanni daban-daban na birnin Tehran, inda su ka nufi dandalin Juyin juya hali da yake a tsakiyar birnin. Manufar yin Zanga-zangar ta yau, ita ce yin tir da tsirarun mutanen da su ka yi tarzoma da kone-konen dukiyoyin al’umma a makon da ya gabata.

Har ila yau masu Zanga-zangar sun daga kwalaye da suke dauke da take na yin tir da Amurka da yan korenta da suka rika nuna goyon bayansu ga mabarnata.

Daga cikin wadanda su ka gabatar da jawabi a wurin gangamin da akwai kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Janar Husain Salami, wanda ya bayyana cewa; Makiya sun bige da haddasa hargitsi ne bayan da Iran din ta gagari su yi fada da ita.

A ranar 15 ga watan Nuwamba da muke ciki ne gwamnatin kasar Iran ta kara farashin man fetur don tallafawa marasa karfi da rarar kudaden karin.

Amma a lokacin da mutane suka fito kan tituna suna nuna damuwarsu da karin farashin, sai wasu yan batagari wadanda suka sami horo daga kasashen waje suka shiga cikinsu suna ta kone-kone motoci, da wuraren jama’a da kuma ofisoshin gwamnati da shagunan mutane. A wasu wuraren an kashe mutane da dama.

Bayan haka ne mutanesuka fara fitowa kan tituna suna yin allawadai da masu tada hankali a wurare daban-daban a duk fadin kasar.

 

3859617

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، hankali ، mutane ، Iran
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: