IQNA

22:25 - December 12, 2019
Lambar Labari: 3484313
Bangaren kasa da kasa, jami’an saron Isra’ila sun yi awon gaba da wasu jagororin kungiyar Hamas.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, rahotanni daga garin Alkhalil na cewa, jami’an saron Isra’ila sun yi awon gaba da wasu jagororin kungiyar Hamas kuma ba a san inda aka nufa da sub a.

Hamas ta bayyana hakan a matsayin wani mataki na tsokana, da nufin ganin ta tunzura Hamas da magoya bayanta da ma sauran al’umma Palastinu domin mayar da martani.

Abdullatif Alqanu mai magana da yawun kungiyar Hamas ya bayyana cewa, dukkanin mutanen da aka kame wadamda aka kame ne a baya wadanda an riga an sake su, shi ne kuma aka sake kame su, wanda ga alama dama hakan tsararren shiri ne.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3863617

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Hamas ، isra’ila ، jagorin
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: