IQNA

12:59 - December 13, 2019
Lambar Labari: 3484314
A yau ma falastinawa za su gudanar da gangami kamar yadda suka saba gudanarwa a kowace Juma’a.

Kamfanin illancin labaran IQNA, falastinawa na shirin gudanar da gangami kamar yadda suka saba gudanarwa a kowace Juma’a a karo na tamanin da hudu.

Babbar manufar wannan gangami da ake gudanarwa a yankin zirin Gaza dai ita ce kara tabbatar da matsayin al’ummar falastine na neman hakkokinsu da aka danne musu saboda zalunci, daga ciki har da dawowar falastinawa ‘yan gudun hijira zuwa kasarsu.

Tun bayan fara wanann gangami da ak yi a kowace juma’a , ya zuwa yanzu mutane da dama ne suka yi shahada, yayin da wasu dubbai kuma suka samu samu raunuka.

Abin tuni a nan dai shi ne, daga lokacin fara wannan gangami ya zuwa yanzu falastinawa 330 ne suka yi shahada, sakamakon hare-haren da Isra’ila take kai wa kan masu gangamin.

 

https://iqna.ir/fa/news/3863725

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، falastinawa ، gangami ، Gaza
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: