IQNA

13:31 - December 17, 2019
Lambar Labari: 3484325

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Mogamad Ganief Ebrahim Hendricks wakilin musulmi a majalisar dokokin Afrika ta kudu ya bayyana nahiyar Afrika da cewa tana dauke da musulmi masu tarin yawa.

Yace addinin mulunci yana da matukar muhimmancia  nahiyar Afrika, domin baya ga kasashen larabawan Afrika, akwai daga cikin kasashen wadanda mafi yawan al’ummominsu musulmi ne.

Haka nan kuma wakilin musulmin a majalisar dokokin Afrika ta kudu ya bayyana cewa, ana samun karuwar musulmi a kasar.

Kamr yadda ya bayyana cewa musulmi suna zaune lafiya da kowa ba tare da wani sabani da sauran al’ummomi ba, duk kuwa da cewa akwai masu nuna kyama ga musulmia  cikin kasar ta Afrika ta kudu.

Ya kuma yaba da yadda gwamnatin Afrika ta kudu take yin mu’amala da musuli ba tare da nuna musu wani banbanci ba.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3862348

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: