IQNA

15:50 - December 30, 2019
Lambar Labari: 3484358
Kungiyar izbullah a kasar Lebanon ta bayyana harin Amurka a Iraki da cewa yunkuri na neman wargaza kasar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin tashar Almanar ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da kungiyar Hizbullah ta fitar, ta bayyana harin da Amurka ta kaddamar kan dakarun sa kai na Hashdu Sha’abi a Iraki da cewa ya tabbatar da Amurka ba zaman lafiyar Iraki take so ba.

Bayanin ya ci gaba da cewa, dakarun Hashdu sha’abi suna wakiltar dukkanin al’ummar Iraki ne, kuma kai musu hari an matsayin kai wa dukkanin al’ummar Iraki hari ne.

Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa, bisa la’akari da cewa wadannan dakaru su ne suka taka gagarumar rawa wajen korar yan ta’addan IS daga Iraki, wannan mataki na Amurka ya nuna cewa ita ce ke mara baya ga ‘yan ta’addan IS.

Daga karshe kungiyar ta yi fatan saun rahmar Allah ga wadanda suka yi shahada sakamakon harin na Amurka, da kuma samun lafiya ga wadanda suka samu raunuka.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3867590

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Hizbullah ، Lebanon ، yunkuri
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: