IQNA

15:53 - December 30, 2019
Lambar Labari: 3484359

An Kawo Karshen Babban Taron Musulmin Kasar Amurka

Bangaren kasa da kasa, an kammala bababn taron musulmin kasar Amurka.

An Kawo Karshen Babban Taron Musulmin Kasar Amurka

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a jiya ne 29 ga watan Disamba aka kawo karshe taron musulmin Amurka na MAS-ISNA a babban dakin taruka na Mccormica Place da ke birnin Chicargo.

Wannan taro dai ana gudanar da shi ne sau daya a kowace shekara, kuma manufar taro ita ce yin dubi kan halin da musulmin Amurka suke ciki, da kuma duba muhimman kalu bale a gabansu da yadda za su fuskanci hakan.

Baya ga haka kuma taron yana yin dubi kan batutuwa da suka shafi makomar rayuwar musulmi a kasar, musamman yara da masu tasowa daga cikinsu.

Taron MAS-ICNA shi ne taro musulmi mafi girma da ake gudanawa a arewacin Amurka, wanda kuma bisa ga al’ada yana gudana ne a karshen watan Disamba na kowae shekara.

Ana gudanar da taron ne a wannan lokaci da ake samun hutu na kirsimati, inda mutane za su iya yin tafiye-tafiye ba tare da wata matsla ba.

Musulmin sukan hadu su tattauna su gana da ‘yan uwansu da abokansu da suke zuwa daga sassa daban-daban na Amurka.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3867523

 

 

captcha