IQNA

19:15 - December 30, 2019
Lambar Labari: 3484361
Bangaren siyasa, Sayyid Abbas Musawi ya ce harin harin Amurka a Iraki goyon bayan ta’addanci ne.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Sayyida Abbas Musawi kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, ya ce babu shakka harin sama da Amurka ta kai Iraki, kan dakarun na Kata’ib Hisbullah da suka yaki kungiyar daesh manuniya ce ta irin yadda Amurka ke goyan bayan ayyukan ta’addanci.

A ranar juma’a da ta gabata ce Amurka ta kai harin sama a wasu sansannonin dakarun kungiyar Kata’ib Hisbullah ta kasar Iraki a yammacin lardin Anbar, inda mutane ashiin da biyar suka rasa rayukansu kana wasu sama da hamsin suka jikkata.

Harin dai a cewar kakakin harkokin wajen kasar ta Iran, ya nuna yadda Amurka take karya da kunfan baki na cewa tana yaki da ta’addanci, duba da harin data kai wa mayakan da suka raunana ayyukan ta’addancin kungiyar IS a kasar ta Iraki.

Mussavi ya kara da cewa, kasancewar sojojin kasashen waje a yankin, shi ne umul’aba’insin matsalar tsaro da rikice rikice, wanda dole ne Amurka ta kawo karshen mamayar da take a yankin.

 

https://iqna.ir/fa/news/3867589

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: