Bayan shekaru masu tsawo yana yin jihadi cikin tsarkin niyya da jarunta a cikin fagagen gwagwarmaya da shaidanu da ashararai na duniya, da kuma wasu shekarun masu tsawo na neman shahada akan tafarkin Allah, a karshe Sulaimani abin kauna, ya kai ga samun wannan matsayin na koli.
Mafi tabewa a tsakanin mutane sun zubar da jininsa mai tsarki.
Muna mika sakon taáziyya da kuma murna ta wannan shahadar mai girma zuwa ga wanzajjen Allah a doron kasa, wanda rayukanmu su ke a matsayin fansa a gare shi, da kuma ruhinsa, haka nan ga alúmmar Iran.
Shi ( Kasim Sulaimani) yana a matsayin kyakkyawan misali ne na wanda ya sami cikakkiyar tarbiyyar musulunci a karkashin koyarwar Imam Khumai, kuma ya tafiyar da dukkanin rayuwarsa ne a fagen jihadi akan tafarkin Allah.
Shahada, tana a matsayin wata gagarumar kyauta ce ta kokari da kwazon da ya yi a tsawon wadannan shekaru. Kuma da yardar Allah da taimakonsa, ayyukan da ya aikata da tafarkinsa ba za su taba tsayawa ba za su ci gaba, amma daukar fansa mai tsanani tana jiran wadanda su ka aikata wannan danyen laifi, da su ka gurbata hannuwansu da jininsa da kuma na sauran shahidai a daren jiya.
Shahid Kasim sulaimani, dan gwagwarmaya ne na kasa da kasa, kuma dukkanin masu son gwgawarmaya suna kaunar ganin an dauki fansar jininsa.
Masoya,-da ma makiya- su san cewa tafarkin jihadi da gwagwarmaya zai kara samun sabon jini a jika, kuma nasara ta karshe tana jiran masu jihadi akan wannan tafarki mai albarka.
Rashin da mu ka yi na kwamanda mai sadaukar da kai, abu ne mai daci a wurinmu,amma ci gaba da yin gwgawarmaya da kai wa nasara ta karshe za su kara wa makasa da wadanda su ka tafka wannan taása bakin ciki.
Al ummar Iran, za ta rika tunawa da kuma daukaka sunan shahidi mai girman matsayi Laftanar Janar Kasim Sulaimani da sauran shahidan da su ka kasance a tare da shi, musamman babban maábocin Jihadin musulunci, Abu Mahdi, Injiniya.
Don haka ina sanar da kwanaki uku na zaman makoki a fadin kasa, ina kuma mika sakon taya murna da kuma taáziyya ga mai dakinsa da ’ya’yansa masu daraja.
Sayyid Ali Khamnei
13/Dey/ 1398
03-01-2020 http://ha.hausatv.com
Allah ya nuna mana ranar da a share zalunci da azzalumai da ga doron kasa,
Sannan nuna rokon Allah ya yi anfani da mu wajen tabbatar da wannan addinin.
Allah ya faranta rayukan mumunai da fitowar mukkulisin bawa mai son kawo gyara a cikin al'umma, wato Allama Sayyid Ibrahim Zakzaky Mazalum.