IQNA

23:39 - January 05, 2020
Lambar Labari: 3484380
Jaridar Guardian ta Ingila ta bayar da rahoton cewa, wasu masana Iraniyawa sun kutsa cikin wani babban shafin gwamnatin Amurka.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Jaridar Guardian ta bayar da rahoton cewa, wasu masana harkokin yanar gizo Iraniyawa sun yi kutse a cikin wani babban shafin yanar gizo na gwamnatin Amurka inda suka sakon daukar fansa a kan kisan Kasim Sulaimani.

Shafin shi ne FDLP wanda a cikinsa ne ake tattaravdukkanin sakonnin Amurka wadanda za a yada ga jama’a kafin a fitar su, inda  a ciki aka saka wani sako na Ayatollah Khamenei bayan an bata dukkanin kalmomin sirri na shiga cikinsa.

Haka nan kuma an saka wani hoto a cikin shafin, wanda ke nuna cewa Trump zai sha matsanancin duka daga daarun kare juyi.

Sakon Ayatollah Khameni da aka saka a cikin shafin na gwamnatin Amurka shi ne, dukkanin wadanda suke da hannua  kisan shahid Sulaimani da wadanda suke tare da shi za su fuskanci martani mai tsanani.

An kuma rubuta a cikin shafin cewa, ba za mu taba ja da ba ya ba wajen ci gaba da bin tafarkin Kasim Sulaimani, na yaki da da azzalumai ‘yan mulkin mallaka a Syria, Yemen, Bahrain, Falastinu da Iraki da ma a sauran kasashen duniya.

3869321

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: