IQNA

Mahangar Wasu ‘Yan Siyasar Birtaniya Kan Kisan Qassem Soleimani

22:31 - January 07, 2020
Lambar Labari: 3484390
Wasu daga cikin ‘yan siyasar kasar Birtaniya sun soki Trump kan kisan Qassem Sulaimani.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, tashar Aljazeera ta baya da rahoton cewa, Jerremy Hant wanda ya kasance sakataren harkokin wajen Birtaniya a tsakanin 2018 zuwa 2019, da Jack Straw, tsohon sakataren harkokin wajen Birtaniya daga 2001 zuwa 2006, sun soki Trump kan kisan Qassem Sulaimani.

Hant ya ce, rashin yin shawara da abokan kawance na Amurka musamman Birtaniya wajen daukar wannan mataki, ya nuna cewa Trump bai dauki kasashen turai da muhimmanci ba.

Shi ma a nasa bangaren Jack Straw ya bayyana a zantawarsa da jaridar Times cewa; wannan matakin da Trump ya dauka, shugabannin Amurka da suka gabata sun guji daukarsa saboda babban hadarin da ke tatatre da shi, amma shi ya yi gaban kansa.

Straw ya kara da cewa; abin da Trump ya aikata zai jefa rayuwar Amurkawa da kuma sauran ‘yan kasashen turai da ma ita kanta Isra’ila a cikin hatsari.

Ya ce bai san ko Trump yana nufin yin amfani da hakan ne ba domin ya ci zabe ai zuwa, idan haka ne kuma to ba a yi lissafi da kyau ba.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3870056

 

 

captcha