IQNA

9:29 - January 08, 2020
Lambar Labari: 3484392
Dakarun kare juyin juya halin muslunci a Iran sun yi luguden wuta a kan sansanin sojin Amurka na Ainul Asad a Iraki.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a daren jiya ne dakarun kare juyin juya halin musulunci a Iran sun kaddamar da munanan hare-hare a tsakar dare a kan sansanonin sojin Amurka a cikin kasar Iraki a matsayin daukar fansa.

Sanarwar da suka fitar dakarun sun ce wannan shi ne mataki na farko daga cikin matakan martanin da za su mayar a kan Amurka dangane da kisan gillar da suka yi wa Sulaimani a daren jumaa.

Daga daga cikin manyan kwamandojin dakarun kare juyi na kasar Iran janar ya bayyana cewa sun harba makaman ne kafin bizne gawar Kasim Sulaimani a daren jiya.

Haka nan kuma dakarun na Iran sun ce suna sanya ido a kan dukkanin wani kai komo na sojojin Amurka a dukkanin yankin gabas ta tsakiya.

Bayanin ya ambaci abubuwa hudu kamar haka:

1 – Babbar Shadaniya ta duniya ta kwana da sanin cewa martanin dakarun kare juyin juya halin muslunci na nan tafe babu makawa.

2 – Muna gargadi kasashen da Amurka ta kafa sansanonin soji a cikin kasashensu da su kwana da sanin cewa, idan wani jirgin Amurka ya taso daga cikin wadanann kasashe ya nufi Iran, to kuwa sansanonin za su fuskanci ruwan makamai masu linzami na Iran.

3 – Ba za mu taba kallon Isra’ila a matsayin wadda ba ta hannu a cikin wannan aikin ta’addanci ba.

4 – Mutanen Amurka kuma muna yi musu nasiha da cewa, su tilasta wa gwamnatinsu da ta janye sojojin kasar daga yankin gabas ta tsakiya, domin kuwa ‘yan uwansu da aka kawo aka jibge rayuwarsu na cikin hadari a kowane lokaci.

Babu wani taimako sai daga Allah mai girma da daukaka.

https://iqna.ir/fa/news/3870122

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: