IQNA

23:41 - January 10, 2020
Lambar Labari: 3484400
Tashar Almanar ta nuna wani faifan bidiyo wanda a cikinsa Shahid Qasim Sulaimani yake magana.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a farkon wannan faifan bidiyon dai Sayyid Hassan Nasrullah ne yake yin magana kan yadda Shahid Sulaimani ya kasance mutum ne mai matukar son ya yi shahada a tafarkin Allah wajen taimaka ma wadanda ake zalunta.

A ci gaban faifan bidiyon kuma Sulaimani ne yake yin magana a kan masaniyar da yake ad ita dangane da Sayyid Hassan Nasrullah, inda ya bayyana shi da cewa mutum ne mai kyakkyawar zuciya, da gaskiya da kuma amana.

Ya ci gaba da cewa, mutane irin Nasrullah a cikin al’umma suna da babban tasiri ne saboda alakarsu da kyakkayawar alakarsu da Allah, uma a kowane lokaci suna masu mika wuya ga lamarin Allah.

Haka nan kuma ya yi ishara da irin sanayyar da ke tsakaninsu tsawon lokaci, wadda ta samo asali ne sakamakon gwagwarmaya da zaluncin masu girman kai na duniya.

Kamar yadda kuma bayyana cewa akwai kyakkyawar danganta tsakanin Sayyid Nasrullah da kuma jagoran Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, wanda akwai tuntubar juna tsakaninsu a kowane lokaci duk kuwa da nisan da ke tsakaninsu.

Shahid Sulaimani dai ya yi shahada nea  daren juma'ar makon da ya gabata, wanda kuma hakan ya sanya jamhuriyar musulunci daukar matakan gaggawa na mayar da martani.

 

https://iqna.ir/fa/news/3870500

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: