IQNA

15:32 - January 11, 2020
Lambar Labari: 3484403
Facebook ya sanar da cewa daga yanzu zai rika cire duk wasu abubuwa da aka saka da suka danganci Kasim Sulaimni.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a cikin wata sanarwa da kamfanin facebook ya fitar a jiya, ya sanar da cewa daga yanzu zai rika cire duk wasu abubuwa da aka saka da suka danganci Kasim Sulaimni ko kuma dakarun kare juyin juya hali na kasar Iran.

Bayanin ya ce kamfanin zai yi aiki dari bisa dari da dokar Amurka wadda ta haramta duk wani abu da ya shafi dakarun kare juyin juya a kasar Iran, kuma zai share duk wani shafi da aka saka wani abu makamancin hakan.

Tun daga lokacin kisan Kasim Sulamini a makon day a gabata, ya zuwa yanzu facebook ya share shafuka na mutane da dama saboda saka hotuna ko labarai da suka shafi Kasim Sulaimani.

 

https://iqna.ir/fa/news/3870747

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: