IQNA

21:18 - January 14, 2020
Lambar Labari: 3484414
Bangaren kasa da kasa, an fitar alkalumman cin zarafin ‘yan jarida a hannun Isra’ila a shekarar da ta gabata ta 2019.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, ma’aikatar watsa labarai ta Palestine ta bayar da bayanin cewa, ‘yan jarida maza  237 da kuma ‘yan jarida mata 71 ne jami’an tsaron Isra’ila suka ci zarafinsu a cikin shekarar da ta gabata.

Baya ga haka kuma, a cewar bayanin na ma’aikatar watsa labaran Palestine, a cikin shekarar da ta gabata Isra’ila ta rufe shafukan yanar gizo guda 160 na kafofin yada labarai.

Kamar yadda kuma mafi yawan ‘yan jaridar da aka ci zarafinsu suna cikin gudanar da aikinsu ne, musamamn ma masu bayar da rahotannia  zanga-zanga da gangamin mutanen Gaza, inda ‘yan jarida da dama suka samu munanan raunuka.

 

https://iqna.ir/fa/news/3871535

 

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: