IQNA

23:55 - January 21, 2020
Lambar Labari: 3484437
Bangaren kasa da kasa, an bude baje kolin kayan tarihin addinai a birnin Iskandariyya na kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA,Ibtisam Khalil shugaban dakin kayan tarihi na birnin Iskandariya ya sanar da  bude baje kolin kayan tarihin addinai a birnin Iskandariyya na addinan yahudawa da kiristoci da kuam musulmi.

Ya ce daga cikin abubuwan da aka kawo a wurin akwai wasu abubuwan da suke komawa zuwa tarihin yahudawa, inda aka ajiye wani abin nika gari na tarihi da aka yi rubutun ibraniyancia  kansa.

Sai kuma kayayyakin tarihi na addinin kirista wadanda aa baje a wurin, da suka hada da kasakai na tarihi da ake ajiye mai a cikinsu.

Baya haka kuma an baje wasu daga cikin kayayyakin tarihi an adinin muslunci a wurin, daga ciki kuwa har da wani dadadden kwafin kur’ani da aka rubuta a cikin shekara ta 674 hijira kamariyya, wato shekaru 767 da suka gabata.

Baya hakan kuma an nuna wasu kayan tarihi da suka hada da fitilu tun na lokacin sarakunan salujikawa, da kuam daular Usmaniyya.

Ibtisam Khalil tare da ministan yawon bude na kasar Masar Khalil Anani suke jagoranci bude wannan baje koli.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3873232

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: