IQNA

Gwamnatin Saudiyya Za Ta Yanke Taimakon Da Take Baiwa Masallatai A Kasashen Ketare

23:54 - January 26, 2020
Lambar Labari: 3484452
Masarautar Saudiyya na da niyyar yanke taimakon da take bayarwa domin daukar nauyin masallatai a wajen kasar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, jaridar Middle East Mirror ta bayar da rahoton cewa, Muhammad Bin Abdulkarim Issa tsohon ministan shari’a na kasar Saudiyya, kuma babban sakataren kungiyar hadin kan duniyar musulmi (Muslim World League) ya bayyana cewa, gwamnatin Saudiyya za ta daina daukar nauyin masallatai a kasashen ketare.

A zantawarsa da jaridar Le Matin Demanche ta  kasar Switzerland, Muhammad Bin Abdulkarim Isa ya bayyana cewa, a halin yanzu suna siririn mayar da batun kula da masallatai ga hukumomin kasashen da masallatan suke ne, inda yanzu haka sun fara magana da hukumomin Switzerland kan batun babban masallacin Geneva.

Ya ce manufar hakan ita ce rage yawan ayyuka da suka shafi kula da masalatai da kasar take, domin kuwa hakan wani abu ne wanda za a iya hada kai da hukumomin kasashe domin aiwatar da shi.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3874269

 

 

 

captcha