IQNA

23:02 - January 27, 2020
Lambar Labari: 3484454
Majalisar dokokin tarayyar turai za yi zama kan dokar hana musulmi zama 'yan kasa a India.

Majalisar kungiyar tarayyar turai za ta gudanar da wani zama domin yin dubi kan daftarin kudirin da ke sukar sabuwar dokar kasar India a kan bayar da hakkin zama ‘yan kasa ga musulmi.

‘Yan majalisar kungiyar tarayyar turai 154 ne suka rattaba hannu kan amincewa da daftarin kudirin yin bincike kan batun, wanda ake sa ran a ranar Laraba mai zuwa ce kungiyar tarayyar turai za ta gudanar da zama, domin yin bahasi kan daftrain kudirin, wanda kuma a ranar Alhamis za ta kada kuri’a a kansa.

Gwamnatin kasar India ta kirkiro sabuwar doka, wadda ta haramta bayar da izinin zama dan kasa ga musulmi daga kasashen musulmi, inda dokar ta amince a bayar da izinin zama dan kasa ga wadanda ba musulmi ba dag akasashen musulmi uku kawai, wato Bangaladash, Pakistan da kuma Afghanistan.

Daftrain kudirin majalisar kungiyar tarayyar turai ya bayyana wannan doka ta gwamnatin kasar India da cewa ta nuna wariya ce ga musulmi.

Wannan doka dai ta jawo zanga-zangar miliyoyin mutanea kasar India, domin yin tir da Allawadai da ita, tare da kiran gwamnatin kasar da ta sake yin nazari kan dokar.

Sai dai a nata bangaren gwamnatin kasar India ta bayyana cewa, ta dauki wannan matakin ne na bayar da izinin zama dan kasa ga wadanda ba musulmi ba kawai daga wadannan kasashe, domin karfafa mabiya addinai marassa rinjaye a wadannan kasashe.

 

https://iqna.ir/fa/news/3874544

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: