IQNA

Tattaunawar Abu Mazin Da Haniyya Kan Shirin Trump A Kan Falastinu

13:50 - January 29, 2020
Lambar Labari: 3484463
Bangaren kasa da kasa, Abu Mazin ya zanta da shugaban kungiyar Hamas Isma’ila Haniyya kan shirin Amurka na mu’amalar karni a kan Falastinu.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar da rahoton cewa, a zantawar ad ta gudana sakanin bangarorin biyu ta wayar tarho, Isma’ila Haniyya ya tabbatar wa Abu Mazin da cewa, Hamas tana tare da shi kuma tana goyon bayansa a kan matakin da ya dauka na yin watsi da shirin Trump.

Haka nan kuma Haniyya ya sheda wa Mahmud Abbas Abu Mazin cewa, dole ne su aiye duk wani sabani da ke tsakaninsu, domin su fuskanci wannan shiri da ke rusa Falastinu baki daya.

Shi a nasa bangare Abu Mazin ya tabbatar wa Haniyya ya zama wajibi a kan dukkanin bangarori na falastinawa da su dunkule wuri guda domin fuskantar wannan shiri na Amurka da Isra’ila.

A nasa bangaren Khalid Batash daya daga cikin jagororin kungiyar Jihadul Islami ya bayyana cewa, wanda ya goyi bayan shirin Trumpa  akn Falastinu, yana matsayin makiyi ne a wurin al’ummar Falastinu baki daya.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3875018

captcha