IQNA

23:55 - February 02, 2020
Lambar Labari: 3484475
An kame wani mutum na shirin fita da wani kwafin kur’ani mai kima daga kasar India.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, a jiya jami’an tsaron lardin Ragistan na kasar India sun kame wani mutum na shirin fita da wani kwafin kur’ani mai kima daga kasar, wanda aka rubuta tun lokacin sarakuna Gukan na India.

Kwafin kur'anin dai an rubuta shi ne tun daruruwan shekaru da suka gabata da ruwan zinari, kuma an kame mutumin mai suna Banwari Meena yana kokarin fitar da shi.

Ya bayyana cewa yana da shirin sayar da wannan kwafin kur'ani nea  kasar Bangaladash a kan kudi da suka kai kimanin rubia miliyan 160.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3875848

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: