IQNA

Netanyahu Ya Gana Da Shugaban Majalisar Shugabanci Ta Kasar Sudan

23:55 - February 03, 2020
Lambar Labari: 3484481
Bnagaren kasa da kasa Firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya gana da shugaban majalisar shugabanci ta kasar Sudan.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, kamfanin dillancin reuters ya bayar da rahoton cewa, ofishin Netanyahu ya fitar da sanarwar cewa, shugaban majalisar shugabancin rikon kwarya a kasar Sudan Abdulfattah alburhan ya gana da Netanyahu a birnin kampala na kasar Uganda.

Bayanin ya ce Netanyahu ya bayyana cewa a halin yanzu Sudan ta kama sahihin tafarki.

Haka nan kuma bayanin ofishin Netanyahu ya tabbatar da cewa, Abdulfattah Alburhan yana da niyyar kulla alaka da Isra’ila.

Netanyahu dai ya kai ziyara ta yini guda a kasar Uganda ne, inda ya bayyana cewa kasar ta Uganda tana da shirin gina ofishin jakadancinta a birnin Quds.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3876319

 

 

 

captcha