IQNA

23:50 - February 07, 2020
Lambar Labari: 3484493
Kotun da ke sauraren shari’a Sheikh Zazaky da mai dakinsa ta sake dage zaman sauraren shari’ar har makon karshe na wannan wata.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, kutun da take sauraron shari’ar da akewa Sheikh Ibrahim Zakzaky da matarsa Zinat a birnin kaduna na tarayyar Najeriya ta gudanar da zaman sauraron shari’ar ba tare da wadanda ake tuhuman sun halarci kotun ba.

Rahotanni sun ce bayan shigowar alkali kotu, wakilan bangarorin biyu wato lauyan gwamnatin jihar Kaduna da kuma na shugaban harka Islamiya a Najeriya sun gabatar da jawabai inda Femi Falana Lauyan sheikh Zakzaky ya bukaci alkalin ya amince da rashin zuwan su kotun, don matar sheikhin malamin ba ta da lafiya, bata iya tafiya don rashin lafiya.

Amma sai alkalin ya tambayeshi ko za su iya zuwa ranar Jumma’a don sauraron wasu Karin tuhumar da ake masu, sai Falana ya ce ba za su iya ba. Sannan ya bukaci a dage karan zuwa ranar 24 da kuma 27 ga watan Febrereun da muke ciki.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3877138

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: