IQNA

Masallacin Bait Rahman a birnin Ache na kasar Indonesia, yana tsohon tarihi na gwagwarmayar al'ummar kasar wajen korar turawan mulkin mallaka na Holland daga kasar. Haka nan kuma saboda yin amfani da kayan gini masu nagarta, gininsa bai rushe ba a lokacin guguwar tsunami a shekara ta 2004.