IQNA

23:55 - March 04, 2020
Lambar Labari: 3484585
Tehran- (IQNA) kwamitin malaman addinin muslunci a  kasar Yemen ya yi tir da Allawadai da kisan musulmi a kasar India.

A wani bayani da kwamitin malaman addinin muslunci a  kasar Yemen ya fitar, ya bayyana kisan musulmi da masu tsatsauran ra’ayin addinin hindu suke tare da taimakon jami’an tsaro da cewa abin ban takaici ne.

Bayanin ya ce abin da ya faru nuna wariya ce da kyama ga musulmi a kasar ta India, wanda kuma gwamnatin kasar ce take da alhakin hakan kai tsaye.

kwamitin malaman addinin muslunci a  kasar Yemen ya ce yana kiran dukkanin musulmi da ma masu kishin ‘yan adam a  duniya, da su taimaka ma musulmin kasar India kan kisan gillar da ake yi musu.

 

3883057

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: