IQNA

23:41 - March 05, 2020
Lambar Labari: 3484587
Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatullah Sayyeed Ali Khamenei ya bukaci gwamnatin kasar Indiya ta kawo karshen kisan kiyashin da ake yi wa Musulman kasar.

Wannan bayani na jagora ya zo ne a shafinsa na twitter inda ya yi Allah wadai da kisan da mabiya addinin Hinbdu suke yi wa Musulman kasar India wanda adadinsu ya kai arbai’in a cikin kwanaki hudu da suka gabata.

Haka nan kuma ya kuma bukaci gwamnatin kasar Indiya ta hana mabiya addinin Hindu masu tsatsauran ra’ayin addini fada wa Musulman kasar.

Sannan kuma ya bayyna cewa zukatan musulmi suna kuna matuka saboda ganin yadda ake yi wa musulman kasar india kisan kiyashi.

Ko a kwanaki uku da suka gabata ma ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi kira ga gwamnatin kasar ta Indiya da ta hada kan mutanen kasar ta kuma daina nuna bambanci a cikin mabiya addinai na kasar da suke rayuwa tare da juna.

 

3883441

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: