IQNA

23:48 - March 05, 2020
Lambar Labari: 3484590
Tehran (IQNA) makamman garkuwa kan hare-haren sama na dakarun kasar sun sake murkushe wasu hare- haren makamai masu linzami na Isra’ila.

Kafofin yada labarai na Siriya sun rawaito cewa makamman garkuwa kan hare haren sama na kasar, sun sake murkushe wasu jerin hare haren makamai masu linzami na Isra’ila a cikin daren jiya Laraba.

Rahoton ya ce an murkushe dukkan hare haren na makiya a kudu maso yammaci da lardin Qouneitra da kuma tsakiyar kasar, kuma an kakkabo dukkan makamman ba tare da sun cimma manufarsu ba.

Wannan yankin Qouneitra dai na da iyaka da tuddan Golan na Siriya da Isra’ila ta mamaye tun shekaru masu yawa.

Haka nan kuma wannan ba shi ne karon farko ba da Isra’ila ke kai ire iren wadannan hare hare kan Siriya ba,

 

3883388

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: makaman ، Syria ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: