IQNA

Daya Daga Cikin Manyan Malamai A Iraki Ya Bukaci A Kori Jakadun Amurka Da Burtaniya Daga Kasar

23:56 - March 08, 2020
Lambar Labari: 3484600
Tehran (IQNA) Ayatollah Jawad Alkhalisi ya bukaci a kori jakadun Amurka da Burtaniya daga Iraki.

Kamfanin dillancin labaran Saumaria News ya bayar da rahoton cewa, Ayatollah Sheikh Jawad Alkhalisi daya daga cikin manyan malaman addini a kasar Iraki ya bukaci a kori jakadun Amurka da Burtaniya daga kasar saboda yada barna da munanan dabiu da suke a tsakanin al’ummar kasar.

Ya ce hakika ofisoshin jakadanci na kasashen Amurka da da Burtaniya da suke a cikin kasar Iraki, suna yada barna a tsakanin alumma musamman ma matasa, inda suke karkatar da su daga koyarwa irin ta addini, wanda hakan ya saba wa dukkanin ka’idodi da yarjejeniyoyi da huldar diflomasiyya.

Malamin ya ce yana yin kira ga mahukunta da su sauke nauyin da ya rataya a kansu na kubutar da Iraki ta hanyar korarar jakadun wadannan kasashe biyu.

 

3883900

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki amurka Burtaniya
captcha