IQNA

15:54 - March 09, 2020
Lambar Labari: 3484602
Tehran (IQNA) firai ministan kasar Sudan Abdullah Hamduk ya tsallake rijiya da baya a yau bayan kai masa wani harin bam a birnin Khartum.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, an kai wa Abdullah Hamduk hari ne ta hanyar tayar da bam a cikin tawagar motocin da suke tare da shi a yau.

Rahoton ya ce biyu daga cikin motocin da suke cikin tawagarsa sun kone da wuta, amma shi ya tsallake, kamar yadda kuma babu wani wanda ya rasa ransa a wurin.

Haka nan kuma rahoton ya kara da cewa, bayan faruwar lamarin, an dauke Hamduk zuwa wani wuri da ba a sani sani domin kula da lafiyarsa da kuma tsaronsa.

3884096

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Abdullah Hamduk ، Sudan ، firai minista ، tsallake rijiya ، da baya ، Khartum
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: