IQNA

23:54 - March 12, 2020
Lambar Labari: 3484614
Tehran (IQNA) ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya aike da wasika zuwa ga babban sakataren majalisar dinkin duniya.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Musawi ya bayar da sanarwar cewa, Iran Muhammad Jawad Zarif ministan harkokin wajen kasar Iran, ya aike da wasika zuwa ga babban sakataren majalisar dinkin duniya kan wajabcin janye wa Iran takunkuman da wasu suka dora mata, domin yaki da corona.

Ya kara da cewa bayan haka kuma Zarif ya aike da wannan wasika zuwa ga wasu daga cikin ministocin harkokin waje na wasu kasashe, domin yi musu bayani kan muhimmancin sakon nasa.

3884938

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: