Kamfanin dillancin labaran KUNA ya bayar da rahoton cewa, kwamitin babban masallacin masallacin birnin Brussels na kasar Belgium, ya sanar da dakatar da sallar Juma’a sakamakon yaduwar cutar corona a kasar.
Bayanin ya ce daukar wannan mataki ya zo ne sakamakon yadda ake samun yaduwar cutar a tsakanin mutanen kasar cikin sauri, wanda hakan zai iya shafar mutane da suke taruwa a cikin masallaci.
Haka nan kuma kwamitin masallacin ya sanar da cewa, an fara gudanar da aikin feshen maganain kwayoyin cuta acikin masallacin da kewaye.
A jiya Laraba gwamnatin Belgium ta sanar da cewa mutane 47 sun kamu da cutar corona, wanda hakan ya daga adadin mutanen da suka kamu da cutara kasar zuwa 314 ya zuwa yanzu.