IQNA

Malamin Yahudawa Ya Yi Bayani Kan Corona Da Kuma Karshen Zamani

23:59 - March 14, 2020
1
Lambar Labari: 3484623
Tehran (IQNA) Alexender Buroda shugaban kungiyar hadin kan yaudawan Rasha ya bayyana cewa babu batun bullar Corona a cikin alamomin karshen zamani.

Tashe Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Alexender Buroda shugaban kungiyar hadin kan yahudawan kasar Rasha ya bayyana cewa bullar cutar corona da matsalolin da tattalin arzikin duniya ya shiga ba su su da alaka da karshen zamani.

Ya ce bai kamata rika danganta duk wani bala'i da karshen zamani ba, domin kuwa akwai abubuwa da addini ya ambata kan karshen zamani, amma wannan baya daga ciki.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa akwai masassarar da za ta bulla a kasar Spain a karshen zamani wadda bayaninta na cikin addini, wadda za ta yi sanadiyyar mutuwar kashi daya bisa uku na dukkanin mutanen nahiyar turai.

Ya ce amma wannan annoba ta corona da ta bulla bata daya daga cikin wadannan abubuwa da aka ambata a cikin addinin yahudanci.

 

3885156

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
nayarda da wannan ba shi nd karhe n duniyaba
captcha