IQNA

23:58 - March 21, 2020
Lambar Labari: 3484643
Tehran (IQNA)an rufe masallacin Sayyida Zainab na wani dan lokaci.

Tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, mahukuntan kaar Masar sun sanar da rufe masallacin Sayyid Zainab da ke birnin Alkahira inda dubban mutane suke gudanar da ziyara a kullum.

Bayanin da mahukuntan suka fitar bayan tattaunawa da malamai kan batun ya nuna cewa, bisa la’akari da halin da ake ciki na tsoron yaduwar cutar corona, ya zama wajibi a rufe wannan masalaci a halin yanzu.

Kafin wannan lokacin ma an rufe wasu masallatan a garin Jurja da ke lardin Suhaj, inda aka rufe masallai 4.

Haka nan shi ma a nasa bangaren Ahmad Tayyib sheikhul Azhar ya bayar da umarnin rufe babban masallacin cibiyar ta Azhar har zuwa wani lokaci nan gaba.

3886718

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: masallatai ، asyyida Zainab ، Masar ، Alkahira ، rufe
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: