IQNA

Za A Rika Saka Karatun Kur’ani Ka Tsaye A Masallatan kasar Mauritania

23:54 - March 23, 2020
Lambar Labari: 3484648
Tehran (IQNA) ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Mauritania ta sanar da cewa za  arika saka karatun kur’ani a masallatan kasar adukkanin rana.

Shafin yada labarai na Alakhbar ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ta fitar, ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Mauritania ta sanar da cewa za  arika saka karatun kur’ani a masallatan kasar adukkanin rana domin samun natsuwa da kuma addu’a kan ibtila’in corona.

Bayanin ya ce za a rika yin amfani da lasifikokin masallatai wajen saka karatun kur’ani a biranen kasar, domin kaskantar da kai ga Allah da ya yaye wa al’umma wannan bala’in da same su.

A kan wanann bau Yaslam Almukarin mai bayar da shawara ga ministan kula da harkokin addini a kasar ya bayyana cewa, tuni a ka bayar da umarnin ga limamai na masallatai domin fara aiwatar da wannan shiri.

Kasar Mauritania dai ta dauki matakai na hana shiga fita  akasar, kamar yadda kuma ta rufe makarantu na addini da na book gami da dakatar da duk wasu taruka na gwamnati da na jama’a baki daya a kasar, domin kaucewa yaduwar corona.

 

3887010

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: mauritania cutar corona kasar
captcha